Sunana Samira,ni haifaffiyar wani gari ce a gabashin arewa.bayan rabuwa ta da mijina nafarko na dawo kano da zama domin samun cikar burina na zama ma’aikaciyar lafia.Sai dai kash,ashe zan gamu da qaddarar da zata gigita rayuwa ta.Ina cikin tafiya a titin zoo rd dake cikin birnin kano,sai ga mota qirar c300 ta sha gabana,cikin sauri naga anbude kofar motar,sai ga wani yafito daga motar,cikkaken namiji ne mai siffar kamala da mutunci,yayi min sallama cikin nutsuwa na amsa shi,yace min sunan sa Muhammad,ya tambaye ni suna na kafin na kai ga amsa shi,ya sake neman izinin ko zan shiga ya qarasa dani gida domin yanaso yasan gidan mu,nan take nace masa aa bazan shiga ba hasali ma ni ina daf da qarasawa gida,sai yace toh dan Allah nayi masa alfarma zaibiyo ni a baya domin yaga gidan,na aminta da hakan na wuce mota na biye dani a hankali har muka iso gida.Isowar mu gida muka tarar da Kawu na a zaune qofar gida na gaishe shi na shigewa ta gida ban tsaya sauraran wannan bawan Allah ba.Ina cikin gida sai naji muryar Kawu yana kwala min kira,Ashe bayan na shigo gida bawan Allah nan fitowa yayi daga mota yazo ya gabatar da kansa wajen Kawu,Sannan yace a bashi izini na fito muyi magana tare da izinin neman aurena,domin shi ba mazaunin kano bane,baqo ne,kuma in shaa Allah yana so kafin ya bar kano a ajiye magana.yadda da ya dawo zaa kai shi mahaifata domin ganawa da mahaifa na,tare da tsayar da maganar aure,dan yanaso nan da 4weeks a daura aure.to be continued 🖊️
Leave a comment